IQNA

Hamas ta yaba da sabon Operation Al-Qassam a Gaza

17:52 - August 30, 2025
Lambar Labari: 3493792
IQNA - Wani babban jami'i a kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palastinu (Hamas) ya mayar da martani kan sabon farmakin da dakarun kungiyar Izzad-Din Al-Qassam, reshen soja na kungiyar suka kai kan yahudawan sahyuniya a zirin Gaza, yana mai cewa tsayin daka a Gaza yana sanya sabbin daidaito ga sahyoniyawan.

A cewar Al-Alam, shugaban kungiyar Hamas Izzat Al-Rishq, ya jaddada a matsayin martani ga fadan da ake ci gaba da yi a zirin Gaza: tsayin dakan mu na sanya sabbin daidaito.

Wadannan kalamai na zuwa ne bayan sabon farmakin da kungiyar Al-Qassam ta kai a zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu 9 har zuwa lokacin hada wannan rahoto, sannan kuma ba a ga wasu sojoji hudu ba.

A cewar wani rahoto da kafar yada labaran yahudawan sahyoniya ta bayar, sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila na fargabar cewa a kalla sojoji hudu ne kungiyar Hamas ta kama a yayin arangamar, kuma ana ci gaba da gudanar da gagarumin bincike domin gano su.

Kafofin yada labaran Isra'ila da ke yada fadan da ake ci gaba da yi sun sanar da cewa lamarin tsaro a unguwar Zeitoun da ke Gaza na daya daga cikin al'amura mafi wahala tun ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Kazalika majiyoyin yahudawan sahyoniya sun ba da rahoton cewa, an sake barkewar kazamin fada tsakanin sojojin gwamnatin kasar da mayakan Hamas a unguwar Zeitoun.

A cewar wadannan kafafen yada labarai, mayakan Al-Qassam Brigades sun shirya kwanton bauna tare da kai wani kazamin hari kan rundunar sojojin Isra'ila a unguwar Zeitoun.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun bayar da rahoton cewa, dakaru masu yawa na Al-Qassam Brigades ne suka shiga aikin na Zeitoun tare da kai hari kan sansanonin sojojin Isra'ila.

A cewar wadannan kafafen yada labarai, jirage masu saukar ungulu na sojoji guda shida da aka aike domin kwashe sojoji sun fuskanci mummunan hari a unguwar Zeitoun.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun sanar da cewa, har yanzu ba a ga wasu sojoji hudu ba, kuma akwai yiyuwar dakarun 'yan adawa sun kame su a rikicin na Zeitoun.

Yayin da a baya kafafen yada labarai suka bayar da rahoton faruwar lamarin tsaro guda uku a yankuna daban-daban, a yanzu an ruwaito cewa wani sabon lamari mai wuyar sha'ani ya afku a wuri na hudu a unguwar Al-Zaytuun.

Kafafen yada labarai sun rawaito cewa, ana gwabza fada kai tsaye da manyan makamai tsakanin mayakan Hamas da sojojin Isra'ila a unguwar Al-Zaytoun.

 

 

4302363

 

captcha