
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta OIC ta fitar, ta bayyana damuwarta kan abubuwan da ke faruwa a Sudan tare da yin kakkausar suka kan yadda ake take hakkin bil adama a lokacin hare-haren da dakarun RSF suka kai kan birnin Al-Fasher a cewar Al-Shorouk.
Kungiyar wacce ke da hedikwata a Jeddah a yammacin Saudiyya, ta yi kira da a tsaya tsayin daka kan hakkin bil adama na kasa da kasa, da tabbatar da kare fararen hula da tabbatar da kai kayan agaji ga masu bukata ba tare da cikas ba, tare da jaddada muhimmancin mutunta tanade-tanaden sanarwar Jeddah da aka rattabawa hannu a ranar 11 ga Mayu, 2023.
Kungiyar ta OIC ta nanata muhimmancin yin shawarwari domin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta na jin kai cikin gaggawa a matsayin share fage na tsagaita bude wuta na dindindin, sannan ta bayyana cewa: Wannan matakin zai taimaka wajen ceto rayukan fararen hula, da rage wahalhalun da al'ummar Sudan ke ciki, da kiyaye hadin kai, 'yancin kai, tsaro, kwanciyar hankali da kuma 'yancin fadin kasar.
A cikin 'yan kwanakin nan, hukumomin Sudan, Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa sun zargi dakarun RSF da yin kisan kiyashi da keta hakkin bil'adama a kan fararen hula" a birnin El Fasher. Wadannan zarge-zargen sun hada da yanke hukuncin kisa, kamawa da kuma tilasta wa mazauna wurin gudun hijira.
Dakarun da suka yi wa birnin kawanya sama da shekara guda suna kai hare-hare a birnin tun ranar Lahadi. Duk da haka, Rundunar Taimakon gaggawa ta musanta wadannan zarge-zargen.
Rahotanni daga Majalisar Dinkin Duniya da majiyoyi na cikin gida na cewa, kimanin mutane 20,000 ne aka kashe a yakin basasar kasar Sudan sannan sama da miliyan 15 sun bar gidajensu a matsayin ‘yan gudun hijira; yayin da bincike da wata jami’ar Amurka ta yi ya kiyasta adadin wadanda abin ya shafa ya kai kusan 130,000.