
A shekarun da kasar Iraki ta kasance cikin kwanciyar hankali, wata rana ta zo da ta sauya tarihin sauti da sautin Alkur'ani har abada. Ranar da “Abdul Basit Muhammad Abdul Samad”, fitaccen almara na tilawa, ya shiga cikin fili mai haske na haramin Imam Musa Kazim (AS); a dai-dai wannan lokacin kamar sama ta kazim ta ja numfashi don jin muryarsa.
Iskar dakin ibadar ya cika da kamshin turaren maziyarta, hasken fitulun da ke cikin dakin, sai kuma rada na hajji. Nan da nan, taron ya zama igiyar ruwa, duk idanuwa suka juya waje guda; wani saurayi mai sanyin fuska da kamannin sama ya shiga. Bayan kammala gaisawa, malam Abdul Basit ya tsaya a gaban haramin, ya lumshe idanunsa, ya yi shiru na wani lokaci; shiru wanda shine share fage na daya daga cikin guguwar karatu a tarihi.
Lokacin da ayoyin farko suka zubo daga maƙogwaronsa na zinare, ba zato ba tsammani wurin ibada ya canza. Sautinsa na musamman ya yi ta kara a cikin iska, da kururuwar tsaffin farfajiyar gidan ya sa kowace aya ta fi armashi sau dubu. Masu ziyara sun yi kuka babu kakkautawa,wasu kuma suna zaune a kasa, suna nitsewa cikin karatun. Kamar dai wannan sautin ya sauko ba kawai cikin kunnuwa ba, har ma a cikin rayuka.
Karatun da Abdul Basit ya yi a aya ta 18 zuwa karshen surar Hashr, da suratu At-Takweer, da ta 27 zuwa karshen suratu Fajr a hubbaren Imam Kazim (AS) haduwa ce ta ruhi. Karatun da ya gudana a gaban malamai kamar su Abu al-Ainin Shaisha da Abdul Fattah Shasha'i da kuma kusa da farfajiyar Imam Musa al-Kazim (a.s.).
Wannan karatun tarihi da ya wuce lokaci da sararin samaniya, ya zama alamar soyayyar Ahlul Baiti (a.s) a cikin zuciyar mafi girman makaranci a duniya
Yanzu, bayan shekaru, a ranar tunawa da zagayowar wannan haziƙi mara misaltuwa, wannan muryar tana nan da rai. A duk lokacin da aka watsa karatun nasa a hubbaren Imam Kazim (AS) kamar Bagadaza na wannan shekarar ta sake rayuwa ta dauke mu cikin hawaye, da kwadayi, da ayoyin sama.
Abdul Basit ya tafi, amma muryarsa ta zama marar mutuwa a tarihi. Muryar da aka zana har abada a cikin zuciyar hubbar Kazim.
An haifi fitaccen malamin kur’ani mai tsarki a kasar Masar a shekara ta 1927 kuma ya rasu a ranar 30 ga Nuwamba, 1988
4320214