IQNA

An yi zaman makoki kan shahadar Ayatollah Khamenei a Indonesia

21:45 - March 02, 2026
Lambar Labari: 3494705
IQNA - An gudanar da zaman makoki game da shahadar jagoran juyin juya halin musulunci a Iran a Iran Ayatollah Khamenei a kasar Indonesia.

Shashen kula da hulda da jama'a na ofishin kula da harkokin al'adu na Jamhuriyar muslunci ta Iran a birnin Jakarta na kasar Indonesia ya sanar da cewa, an gudanar da zaman makoki game da shahadar jagoran juyin juya halin musulunci a Iran a Iran Ayatollah Khamenei.

Jakadan kasar Irana  kasar Indonesia Muhammad Burujardi ne ya jagoranci zaman makokin, wanda ya samu halartar jama'a da dama daga sassa na al'ummar kasar ta Indonesia da kuma Iraniyawa mazauna kasar, gami da wasu 'yan kasashen kertare.

A yayin zaman taron makokin an yi addu'oi da karatun kur'ani mai tsarki da kuma bayanai kan rayuwarsa da irin gudunmawar da ya baiwa addini da kuma al'umma.

 

4337893

captcha