IQNA

An Kirayi Majalisun Musulmi Da Su Taka Rawa Wajen Kawo Karshen Cutar Da Musulmi

21:25 - February 20, 2014
Lambar Labari: 1377679
Bangaren kasa da kasa, An kirayi majalisun dokoki na kasashen musulmi da su safke nauyin da ya rataya akansu wajen kare sauran musulmi da suke fuskantar matsin lamba a wasu kasashe na duniya kasantuwarsu marassa rinjaye va cikin wadannan kasashe.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a zantawar da ta hada shi da shugaban majlaisar dokokin kasar Sudan Fatih Izzuddin Mansur a taron shugabannin majalisun dokoki na kasashen muusulmi a birnin Tehran ya bayyana cewa, halin da ake ciki yanzu na lizimta wa majalisun dokoki na kasashen musulmi da su safke nauyin da ya rataya  akansu wajen kare sauran musulmi da suke fuskantar matsin lamba a wasu kasashe na duniya kasantuwarsu marassa rinjaye ko marassa tasiri na siyasa.
A bangare guda kuma wasu suna ganin tsoma bakin da kasashen yammaci suke yi cikin siyasa da harkokin gudanarwa kasashen yankin, musamman shigowar sojojin Faransa da Amurka da sunan fada da ta’addanci, shi ma ya taimaka wajen yaduwar rashin tsaron. A matsayin misali harin da kasashen suka kai kasar Libiya da kifar da tsohuwar gwamnatin kasar hakan ya taimaka wajen yaduwar makamai a yankin.
Don haka masanan suke ganin matukar dai gwamnatocin wadannan yankin suna son fada da ta’addanci da rashin tsaro a kasashen na su wajibi ne suke yi la’akari da wadannan abubuwa da kuma tunanin hanyar magance su.

1376651

Abubuwan Da Ya Shafa: sudan
captcha