Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alakhbar.info cewa, Al'ummar kasar Murtaniya sun gudanar da zanga-zangar nuna bacin ransu kan yadda wasu suka ci mutuncin Alku'ani mai kirma a kasar.
A nasa bangaren kamfanin dillancin labarai na kasar Masar Ya habarta cewa a yau din nan Litinin Al'ummar Birnin Nuwakchot babban birnin Murtanya sun gudanar da zanga-zanga don nuna bacin ransu kan yadda wasu Mutane suka shiga Massalaci a birnin Nuwaktoch sannan suka ciccira Alkur'anan dake cikin wannan Masallaci.
Masu zanga-zangar dai sun rufe manyan titunan birnin na Nuwakchot inda da kel jami'an 'yan sanda suka tarwatsa su sannan suka bude titunan. A daren jiya lahadi ne dai wasu Mutane guda 4 wadanda ba a kai ga gane ko su waye ba suka shiga cikin wani Masallaci dake anguwar Tayarat a arewacin Nuwakchot babban kasar sannan kuma suka ciccira dukkanin ku'anan dake cikin wannan Masallaci sannan kuma suka zubar da shi a kasa.
Ko A ranar 3 ga watan janairun da ya gabata ma, jami'an 'yan sanda na birnin Nawazibu dake arewa maso yammacin kasar sun kama Muhamad wul sheikh kan zarkinsa da cin zarfin Ma'aikin Allah tsira da amincin ... su tabbata a gareishi tare da iyalan gidan tsarkaka.inda Ma'aikata mai kula da harakar Musulinci a kasar ta bukaci Limaman juma'a na kasar baki daya da su kebe wani bangare daga cikin hudubobin nasu na juma'a don yin …. Ga masu son cin zarafin ma'akin…sanadiyar hakan dai Al'ummar kasar sun yi ta gudanar da zanga –zanga don yin ….wadai da wannan Mutune tare da duk wasu masu yunkurin yin batanci tare da cin zarafin musulinci a Duniya baki daya.
Murtaniya dai kasa ce daga yammacin Afirka kuma tan a da Mutane kimanin million 3 da rabi kuma dukkaninsu musulmi ne.