A cewar kafar yada labarai ta Gabas ta Tsakiya, ba a fitar da cikakken bayani kan shirin Amurka na Gaza ba bayan ganawar, sai dai Donald Trump ya bayyana shi da cewa yana da kyau bayan ya bar taron, yayin da shi ma shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kira taron mai matukar fa'ida.
A gefen taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80, Trump ya yi wata ganawa da shugabannin kasashen Larabawa da na Musulunci, wanda a cewar kamfanonin dillancin labarai, ya samu halartar manyan jami'ai daga Qatar, Masar, Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Jordan, Turkiyya, Indonesia da Pakistan.
A farkon taron, Trump ya bayyana taron a matsayin mai matukar muhimmanci sannan ya kara da cewa: "Muna neman kawo karshen yakin zirin Gaza da kuma mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su."
Da yake bayyana taron a matsayin mafi muhimmanci taron da ya yi a ranar Talata, ya ce gwamnatinsa na shirin mayar da mutanen Isra'ila 20 da aka yi garkuwa da su da gawarwaki 38 daga Gaza.
Bayan kalaman na Trump, Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya kuma ce: Halin da ake ciki a Gaza ba shi da kyau kuma muna nan don yin duk abin da za mu iya don kawo karshen yakin da kuma mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su.
Ya kara da cewa: "Muna dogara ga shugabancin Trump don kawo karshen yakin Gaza."