IQNA

Kasar Morocco Ta Bayar Da Kyautar Kur'anai 10,000 Ga Masallatan Gabon

23:26 - March 08, 2014
Lambar Labari: 1384485
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Moroco ta bayar da kyautar kur'anai da suka kai kimanin kwafi 10,000 ga masallatan kasar Gabon da nufin kara fadada fahimta ta alkur'ani mai tsarki a tsakanin al'ummar kasar musamman ma musulmi daga cikinsu.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Lematin cewa, akasar Moroco ta bayar da kyautar kur'anai da suka kai kimanin kwafi dubu goma ga masallatan kasar Gabon da nufin kara fadada fahimta ta alkur'ani mai tsarki a tsakanin al'ummar kasar musamman ma musulmi daga cikinsu wadanda suke da bukatar karin masaniya a kansa da koyarwarsa.
Wannan ya zo ne a lokacin da sarkin kasar ta Morocco yake gudanar da wata ziyara a kasar ta Gabon, inda ya ziyarci masallatan kasar tare da ganawa da shugabannin musulmi, da kuma jin irin matsalolinsu da kuma abubuwan da suke bukata daga Morocco ta taimaka musu.
An gudanar da bababn taron ne a masallacin Hassan na biyu da ke birnin Librivelle fadar mulkin kasar, wanda sarkin ya gina da nufin daukaka musulunci a kasar, taron kuma ya samu halartar wasu daga cikin jami'an gwamnatin kasar.

1383984

Abubuwan Da Ya Shafa: Gabon
captcha