IQNA

Jami’an Tsaron Kasar Somalia Sun kai Samame A Makarantun Kur’ani

21:56 - March 18, 2014
Lambar Labari: 1388737
Bangaen kasa da kasa, jami’antsaron kasar Smaia sun ka samame a wata makarantar koyar da karatun kur’ani mai tsarki a ckin Birnin Magadishou fadar mulkin kasar bias zargin cewa wasu daga cikin malaman makarantar suna cikin ‘yan ta’adda

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa, a sintirin da suke yi , jami’antsaron kasar Smaia sun ka samame a wata makarantar koyar da karatun kur’ani mai tsarki a ckin Birnin Magadishou fadar mulkin kasar bias zargin cewa wasu daga cikin malaman makarantar suna cikin mayakan kungiyar Alshabab.
Gwamnatin kasar Somalia ta ce dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka da ke gudanar da ayyukansu a kasar suna samun gagarumar nasara wajen fatattakar mayakn 'yan kungiyar Alshab da ke dauke da makamai.
A cikin wani bayani da gwamnatin ta Somalia ta fitar a jiya, ta tabbatar da cewa dakarun na tarayyar Afirka sun samu nasarar kwace iko da wasu da dama daga cikin yankunan kudu maso yamma na kasar, wadanda ke karkashin iko kungiyar Alshab, bayanin ya ce dakarun na Afirka sun kara samun wannan nasara ne daga lokacin da dakarun kasar Ethipia suka fara taimaka musu.
A cikin shekara ta 2011 ce mayakan na kungiyar Alshabab suka fara shan kashi a hannun dakrun kungiyar tarayyar Afirka a yankunan da suka kwace iko da su a kudanci da yammacin kasar, duk kuwa da cewa har yanzu akwai wasu kauyuka da ke hannun mayakan kungiyar ta Alshabab da ke da alaka da Alkaida.
1388009

Abubuwan Da Ya Shafa: somali
captcha