Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, letempsds cewa, a cikin wannan mako an zabi sabbin kwamitin bincike na jami’ar Azhar da ke birnin Alkahira a kasar Masar a ci gab ada gudanar da garanbawul da ake yi vabnagarori da daman a jamiar da nufin kyautata ayyukan jami’ar mafi girma a kasashe musulmi.
A wani rahoton kuma an bayyana cewa jami’an tsaron Masar sun kashe magoya bayan kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood ta kasar guda biyu a yau Juma’a, jami’an tsaron Masar sun kai farmaki kan magoya bayan kungiyar ‘yan uwa musulmi a garin Tanta da ke lardin Al-Gharbiyya a arewacin kasar a daidai lokacin da suke shirin fara gudanar da zanga-zangar lumana da suka saba gudanarwa kowace ranar Juma’a kafin sallar Juma’a, inda jami’an tsaron na Masar suka harbe mutane biyu daga cikinsu har lahira tare da jikkata mutum guda.
Tashe-tashen hankula sun kunno kai ne a kasar Masar tun bayan da sojojin kasar suka kifar da gwamnatin Muhammad Morsi na kungiyar ‘yan uwa musulmi a shekarar da ta gabata, kuma mahukuntan kasar da suke samun goyon bayan sojoji suna daura alhakin tashe-tashen hankulan ne kan magoya bayan kungiyar ta ‘yan uwa musulmi.
1392995