IQNA

An Sahyuniyah A Matsayin Tushen Ayyukan Ta'addancin Takfiriyyah

13:48 - July 01, 2014
Lambar Labari: 1424726
Bangaren kasa da kasa, an bayyana yahudawan sahyuniya a matsayin wadanda suke da hannu wajn haifar da kungiyoyin 'yan ta'adda da suke gudanar ayyukansu da sunan addini bisa akida takfiriyyah.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangarensa da ke nahiyar Afirka cewa, wani masani kan harkokin addinai mai suna Taufiq Albanuri cewa, yahudawan sahyuniya ba su ne suke da hannu kai tsaye wajen kafa kungiyoyin takfiriyyah.

A wani labarin na daban kuma kungiyar daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish ta shelanta kafa daular Musulunci tare da sanar da shugabanta Abubakar Baghadadi a matsayin shugaban musulmin duniya.
A jawabin da Abu-Muhammad Adnani kakakin kungiyar Da’ish ya fitar a jiya Lahadi yana dauke da cewa; Manyan mashawartan kungiyar Da’ish sun sanar da kafa daular Musulunci ko kuma Khilafa Islamiyya tare da gudanar da mubaya’a ga Ibrahim Awwad Ibrahim Al-Badri Al-Samarra’i da aka fi sani da Abubakar Baghadadi dan shekaru 43 a duniya a matsayin khalifan musulmin duniya.
Jawabin ya kara da cewa; daga yanzu an maye gurbin daular Musulunci a Iraki da Sham da sunan daular Musulunci ta duniya karkashin khalifancin  Abubakar Baghadadi, kuma wajibi ne a kan dukkanin musulmin duniya su yi masa mubaya’a tare da taimaka masa.
Wannan mataki na kungiyar Da’ish ya bayyana a fili karara cewa; kungiyar ta yi tawaye ga babban kungiyar ta’addanci ta Al-Qa’ida karkashin jagorancin Aiman Al-Zawahiri da ya karbi ragamar shugabancin kungiyar Al-Qa’ida a bayan mutuwar Usama bin Ladan.
1423619

Abubuwan Da Ya Shafa: Takfir
captcha