IQNA

An Bude Wata Cibiyar Mai Suna Safinat Al-Najat A kasar Senegal

18:54 - July 03, 2014
Lambar Labari: 1425419
Bangaren kasa da kasa, an bude wata cibiyar addininmuslunci ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a kasar Senegal da nufin bunkasa ayyukan na isar da sakon addini.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labaransa Afirka cewa, Malam Dawud Sidi ya bude wata cibiyar addininmuslunci ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a kasar Senegal da nufin bunkasa ayyukan na isar da sakon iyalan gidan manzo.

Wasu rahotanni kuma na daban sun sheda cewa fFiye da mutane dari biyu da hamsin ‘yan kasar Senegal mazauna kasar Afirka ta tsakiya suka isa birnin Dakar a jiya, bayan da guje wa tashe-tashen hankulan da ke faruwa a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, wanda ya lakume rayukan mutane fiye da dubu dayta a cikin ‘yan makonni.
Kamfanin dillancin labaran Shin Hawa na kasar sin  ya bayar da rahoto daga birnin Dakar na kasar Senegal cewa, ‘yan kasar su dari biyu da hamsin ne suka safka a filin girgin sama da ke birnin, inda shugaba Macky Sally a tarbe su, daga cikinsu kuwa har da mata da kananan yara.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai a filin jirgin, shugaban na Senegal ya bayyana cewa, yana goyon bayan ‘yan kasarsa da suke zaune a kasar Afirka ta tsakiya da suka yanke shawar komowa gida domin tsira da rayukanu, tare da yin fatar samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a jamhuriyar Afirka ta tsakiya.
1424907

Abubuwan Da Ya Shafa: Sengal
captcha