IQNA

Palastinawa Fiye Da 355 Ne Suka Yi Shahada A Gaza

20:22 - July 21, 2014
Lambar Labari: 1431849
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga yankin Zirin Gaza na Palastinu sun ce adadin palastinawan da suka yi shahada ya haura 355 a cikin kwanaki sha daya, sakamakon hare-haren da jiragen yakin Israila suke kaddamarwa kan al'ummar yankin.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar giz na PressTV cewa, Majiyoyin asibiti a yankin na Gaza sun tabbatar da cewa, daga cikin mutane fiye da 340 da suka yi shahada sakamakon hare-haren Isra'ila, kimanin 75 daga cikinsu kananan yara ne, yayin da wasu fiye da 2400 suka samu raunuka, wasu daga cikinsu na cikin halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai.
A nata bangaren rundunar sojin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta tabbatat da mutuwar biyu daga cikin sojojinta da suka hada har da wani mai babban mukami a cikinsu, sakamakon harin da palastinawa 'yan gwagwarmaya suka kai kan motocinsu masu sulke, a lokacin da suke kokarin shiga cikin yankin Zirin Gaza ta kasa, yayin da bayanin ya tabbatar da cewa wasu sojojin 6 sun samu munanan raunuka.
A cikin wani bayani da mayakan Kata'ib Izzuddin Kassam reshen soji na kungiyar Hamas suka karanta a daren jiya, sun ce sun kame sojan Isra'ila a wani kwanton bauna da suka yi wa wasu motocin sojin Isra'ila masu sulke suka kutsa kai a yankin Tuffah da ke gabacin Zirin Gaza, kuma yanzu haka yana hannu.
1431101

Abubuwan Da Ya Shafa: Palstine
captcha