
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alkhabar cewa, a kasar an girma dukkanin wadanda suka nuna kwazo a wannan gasa a dukkanin bangarorin da aka gudanar da ita kamar dai yadda aka saba a kowace shekara.
A wani labari na daban ministan sifiri na kasar Algeria ya Ammar Goul ya isa birnin wagadugu babban birnin kasar bokina faso a safiyar yau Asabar, kamfanin dillancin labarai chinhuwa na kasar sin ya bayyana cewa ghoul zai gana da shugaban kasar Campore kafin ya isa mahallin da jirgin saman kasar ta Algeria ya fadi a ranar Alhamis da ya gabata.
Gwamnatin kasar ta Borkina Faso ta tabbatar da cewa kungiyoyi da kuma kasashen da dama sun shirya don fara bincike kan faduwar jirgin. Sannan a yau ne ake saran jami’an gwamnatin kasar Faransa da kuma Majalisar dinkin duniya da kuma kasar Mali zasu fara bincike cikin musabbin faduwar jirgin.
Har’ila yau dangin wadanda suka rasa rayukansu a jirgin zasu ziyarci yankin da jirgin ya fadi kilomita 50 daga kan iyaka da kasar Mali.
1433309