IQNA

Afirka Ta Kudu Ta Yi Kira A Kawo Karshen Yakin Gaza

13:51 - August 05, 2014
Lambar Labari: 1436237
Bangaren kasa da kasa, a I gaba da kiran da ake yin a kawo karshen yakin Gaza, mahukunta a bangaren diplomasiya a Afirka ta kudu sun jadda wajabcin kawo akrshen zubar da jinin fararen hula daIsra'ila ke yia yankin zirin gaza.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, Afirka ta kudu ta bukaci kawo karshen kisan mutanen Gaza ba tare da bata lokaci ba, tawagar wakilan gwamnatin kasar ta gana da jami’an kungiyar hadin kan kasashen Larabawa kan batun neman hanyar kawo karshen mummunan halin da ake ciki a yankin Zirin Gaza.
Tawagar wakilan gwamnatin Afrika ta Kudun ta gana da Muhammad Subaihi mataimakin babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a birnin Alkahira na kasar Masar, inda bangarorin biyu suka tattauna batun hanyar tabbatar da shirin dakatar da bude wuta a yankin Zirin Gaza.
Har ila yau tawagar ta gwamnatin Afrika ta Kudu ta jaddada batun kawo karshen killace yankin Zirin Gaza da aka yi tsawon shekaru tare da bayyana shirin gwamnatin Afrika ta Kudu na karbar dawainiyar jinyar kananan yaran da suka samu raunuka sakamakon hare-haren ta’addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan yankin Zirin Gaza.
1435625

Abubuwan Da Ya Shafa: Afric
captcha