IQNA

An Shirin Bayar Da Kammala Horo Ga Daliban Addini A Madagascar

13:57 - August 05, 2014
Lambar Labari: 1436240
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taro na bayar da horo ga wasu daliban makarantar Imam Sadiq (AS) da ke kasar Madagascar dangane da yadda ake gudanar da jawabi na addini.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa a jiya ne aka kammala gudanar da wani taro na bayar da horo ga wasu daliban makarantar Imam Sadiq (AS) da ke kasar Madagascar dangane da yadda ake gudanar da jawabi na addini a gaban jama'a.
Babbar manufar gudanar da wanann shiri na horon ga daliban shi ne samar da mutane masu himma wajen gudanar da ayyukan addini da kuma fadakar da mutane dangane da koyarwar addini, musamamn ma atsakanin mutanen kasar wadanda akasrinsu ba mabiya addinin muslunci ba ne, wadanda suke da kishirwar sanin wani dangane da muslunci.
Malaman da suke koyar da daliban ne suka dauki nauyin shirya taron bayar da horon da kuma gudanar das hi, inda ake ganin cewa hakika ya yi bababn tasiri ta yadda yanzu haka wasu daga cikin daliban sun samu horon da ake bukata domin da wannan gagarumin aiki na addini.
1435797

Abubuwan Da Ya Shafa: Madagascar
captcha