Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarat cewa, ya naklto daga shafin Al-wifag cewa, Sheikh Haisam Salman ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da matakin da mahukuntan kama karya na kasar Bahrain suke dauka na hada malaman shi'a a kasar gabatar da duk wani jawabi domin akuce wa fadakar da al'ummar kasar dangane da hakkokinsu da aka tauye musu kuma ake zaluntar su.
Wata kotu a kasar Bahrain ta yanke hukuncin dauri a gidan kurkuku kan wasu fararen hula 29 sakamakon fafatukar da suke yi na neman gudanar da gyara a harkar siyasar kasar.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bada labarin cewa; Wata kotu a kasar Bahrain a yau Laraba ta yanke hukuncin daurin shekaru goma kan mutane 26, yayin da ta daure wasu mutane uku na daban shekaru uku a gidan kurkuku kan zargin hannu a kai hari kan wani ofishin ‘yan sanda a kasar.
Mutanen 29 sun yi watsi da zargin da jami’an ‘yan sanda ke yi kansu a gaban kotun, amma kotun ta ki saurarensu saboda rahoton da rundunar ‘yan sandan kasar ta gabatar kan su tare da shaidar furucin da ta tatsa daga gare su ta hanyar tursasawa a lokacin da suke tsare a wajen ‘yan sanda.
1437229