IQNA

Dole Isra'ila Ta Kawo Karshen Mamamayr Yankunan Palastinawa

23:50 - September 03, 2014
Lambar Labari: 1446587
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa dakasa ta ce dole ne haramtacciyar kasar Isra'ila ta kawo mamayar yankunan palastinaw da take baki daya.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, Amnesty International da ke kare hakkin bil adama ta kasa tace dole ne haramtacciyar kasar Isra'ila ta kawo mamayar yankunan palastinaw da take bak i daya ba tare da wani bata lokaci ba.

Kungigar Amnesty International ta bukaci da a gudanar da bincike dangane da hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai kan ma'aikatan bayar da gaji a yankin Zirin gaza.  
A cikin wani bayanin da kungiyar ta Amnesty International ta fitar a jiya, ta bayyana cewa akwai bukatar binciken gaggawa dangane da bayanai da ke cewa sojojin Isra'ila sun kai munanan hare a kan asibitoci da kuma motocin daukar marassa lafiya, tare da kashe likitoci da kuma masu gudanar da ayyukan agaji, kamar yadda wasu shedu masu karfi suka tabbatar da cewa sojin Isra'ila sukan hana kai dauki ga mutanen da ta kai wa hare-hare.
A jiya ne haramtacciyar kasar Isra'ila ta ci gaba da kaddamar da hare-harenta kan al'ummar gaza bayan karewa wa'adin tsagaita bude wuta na kwanaki uku, inda daga jiya zuwa ta kashe palastinawa 6, uku da cikinsu kananan yara.
Shugaban kasar tunisia ya fadi cewa, akwai wasu daga cikin shugabanni da sarakunan larabawa da suka nuna rashin amincewarsu da shirin dakatar da bude wuta a Gaza, yana mai yin ishara da cikakken goyon bayan da Isra'ila take samu daga wasu shugabanni da sarakunan larabawa a wannan yaki.
1445787

Abubuwan Da Ya Shafa: palastinu
captcha