
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alharam cewa, an dauki sautin kira’a na Tariq dan marigayi Abdulbasit Abdulsamad fitaccen makarncin kur’ani na duniya wanda ya rayu a kasar Masar kuma ake tuna shi tare da bin salon kira’arsa a dukkanin duniyarmu ta yau.
Wannan karatu an kamala daukarsa tare da bayyana cewa dukkanin malamai a dukkanin cibiyoyin ilimi na kur’ani musamman a cibiyar Azhar an amince da ita, kuma an yarda a watsa ta a dukkanin gidajen radiyo da na talabijin na kasar Masar, wanda hakan zai bayar da dama ga dukkanin cibiyoyin kur’ani na duniya su yi amfani da wannan kira’a.
Bayanin ya ci gaba da cewa Tarik Abdulbasit Abdulsamad ya yi wanan karatu ne da kir’ar warsh, kamar yadda ya yi wata kafin wannan wadda ya safke kur’ani da it a cikin kira ta Hafs bin Asim, kuma ita ake amfani da ita tare da amfana da sautinsa a dukkanin fagage na karatun kur’ani mai tsarki a masar da kuma duniya baki daya.
1450928