IQNA

An Gudanar Da Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki A Afirka Ta Kudu

10:18 - September 19, 2014
Lambar Labari: 1451368
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar karatun kur’ani da kuma harda a kasar Afirka ta kudu tare da halartar makaranta da kuma mahardata daga fadin kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-bilad ta kasar Saudiyya cewa, a jiya an kammala gudanar da gasar karatun kur’ani da kuma harda a kasar Afirka ta kudu tare da halartar makaranta da kuma mahardata daga birane daban-daban na fadin kasar ta Afirka ta kudu.
Bayanin ya ci gaba da cewa mahardata kur’ani mai tsarki 200 ne daga garuruwan kasar suka samu halartar wannan gasa, kuma an gudanar da ita ne a matakai daya bayan daya kamar dai yadda aka saba  yi a kasashen duniya, inda daga karshe kuma aka fitar da wadanda suka zo a matakai na daya da na biyu da kuma na uku a dukkanin matakan gasar, inda aka ba su kyautka na musamman.
An gudanar da wannan gasa ne a birnin Kapetown da ke kudancin kasar, inda babban jami’I mai kula da harkokin addinin muslunci daga bangaren ma’aikatr shari’a  akasar ya jagoranci gabatar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka nuna kwazo, haka nan kuma an gabatar da jawabai ga mahalarta taron na kamala gasar karatun kur’ani, tare da bayyana irin ci gaban da aka samu a kasar ta wannan fuska, duk kuwa da cewa kasar kasa ta mabiya addinin kirista, amma addinin muslunci yana ci gaba da samun karbuwa.
1450730

Abubuwan Da Ya Shafa: S/Afirka
captcha