
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga jaridar Yaum Sabi ta kasar masar cewa, daya daga cikin fitattun malamai a wannan cibiyar ta Azahar Sheikh Ahmad Karimah ya soki salon da cibiyar Azahar take bi wajen koayr da mazhabobin muslunci a bangaren koyarwarta na jami'a, tare da bayyana hakan da cewa akwai kure a cikinsa.
Shehin malamain dai ya fuskanci matsaloli tare da malaman jami'ar Azahar a cikin makon da ya yi wata tafiya zuwa kasar Iran, inda ya gana da manyan malamai na mazhabar Ahlul bait, lamarin da ya sanya jami'ar daukar mataki na gudanar da bincike a kansa, daga bisani kuma aka sanar da dakatar da koyarwar a bangaren shari'a kamar yadda ya saba, bisa hujjar cewa ya gana da malaman shi'a.
Sheikh karima ya ce abin mamaki shi ne yadda jami'ar Azahar ta dauki dukaknin mamzhabobi tana koyar da su hard a mazhabar khawarijawa, wadanda kowa ya yi imanin cewa akidunsu sun hannun riga da koyarwar addinin muslunci, amma duk da haka cibiyar Azahar ta mayar da wannan mazhaba daga cikin mazhabobin da ake koyarwa,a cikin masar hard a wajen kasar.
Ya kara da cewa shi da kansa jami'ar Azahar ta tura shi zuwa kasar Oman domin koyar da wanann mazhaba ta khawarijawa har tsawon shekaru shida, kuma ya yi hakan duk da cewa ya san abin da ke ciki ya saba wa shari'a, kma bai yarda da shi ba, ya ce wannan babban kure da Azhar take tafkawa, kuma idan tana son mutuncinta ya wanzu ta sake yin nazari kan wanann banbanci da take nunawa tsakanin mazhabobin musulunci.