IQNA

21:30 - October 08, 2014
Lambar Labari: 1458532
Bangaren kasa da kasa, an bude wata makarantar koyar da karatun kur'ani mai tsarki a birnin Nuwakshout na kasar Mauritaniya wadda za ta dauki nauyin koyar da yara kanana.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-sharq cewa, a cikin wannan mako an bude wata makarantar koyar da karatun kur'ani mai tsarki a birnin Nuwakshout na kasar Mauritaniya wadda za ta dauki nauyin koyar da yara da shekarunsu ke kasa da goma.

Shugaban huumar da ke kula da ayyukan jin kai a kasar Qatar Shekh Thani Bin Abdullah shi ne ya dauki nauyin gudanar da aikin bude wannan makaranta, inda aka kashe kudade masu yawa da nufin kara bunkasa harkokin kur'ani mai tsarki a kasar musamman ma a tsakanin kanan yara masu tasowa, wanda hakan zai bar tasiri mai kyau a cikin rayuwarsu.

Kasar Mauritaniya na daga cikin kasashen yammacin nahiyar Afirka kuma daya daga cikin kasashen larabawan yankin magrib, wadda al'ummomin kasar suke byar da muhimamnci matuka ga harkokin kur'ani mai tsarki, musamman ma a bangaren harda da karatu, inda sukan taka gagarumar rawa a cikin gasar kasa da kasa da ake gabatarwa a kasashen musulmi.

Fiye da kashi 90 cikin dari na daliban da za su kasance a wannan makaranta dai yara masu riko da koyar addini da ke lizimtar masallatai da wuraren karatun kur'ani da wasu wurare na ibada.

1458108

Abubuwan Da Ya Shafa: Mauritaniya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: