Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Alwasat cewa jami’an masarautar Bahrain da ke tsananin adawa da mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar sun rusa wani alamin Ashura da aka kafa a shirin fara juyin da ake yi nan ba da jimawa ba kamar dai yadda aka saba yin haka daruruwan shekaru da suka gabata a kasar.
Wasu rahotannin kuma sun wata kotu a kasar ta Bahrain ta yanke hukuncin dauri a gidan kurkuku kan wasu fararen hula 29 sakamakon fafatukar da suke yi na neman gudanar da gyara a harkar siyasar kasar.
Kamfanin dillancin labaran faransa ya bada labarin cewa; Wata kotu a kasar Bahrain a yau Laraba ta yanke hukuncin daurin shekaru goma kan mutane ashirin da shida yayin da ta daure wasu mutane uku na daban shekaru uku a gidan kurkuku kan zargin hannu a kai hari kan wani ofishin ‘yan sanda a kasar.
Mutanen ashirin da tara sun yi watsi da zargin da jami’an ‘yan sanda ke yi kansu a gaban kotun, amma kotun ta ki saurarensu saboda rahoton da rundunar ‘yan sandan kasar ta gabatar kan su tare da shaidar furucin da ta tatsa daga gare su ta hanyar tursasawa a lokacin da suke tsare a wajen ‘yan sanda.