IQNA

Kai Hari Kan Husainiyar “Yan Shi’a A Ihsa Aiki Ne Na Jahilci Da Kiyayya

22:36 - November 08, 2014
Lambar Labari: 1471125
Bangaren kasa da kasa, babban maamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Isa Kasim ya bayyana harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai kan masu gudanar da taron Ashura a yankin Ihsa na kasar saudiyya da cewa ya zo bisa mummunan jahilci da kiyayya daga maharani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Radiyo Nur cewa Ayatollah Isa Kasim babban maamin addinin muslunci na kasar Bahrain ya bayyana harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai kan masu gudanar da taron Ashura a yankin Ihsa na kasar saudiyya da cewa ya zo bisa mummunan jahilci na ‘yan ta’addan da neman haddasa fitina.
Jami’an tsaron Sudiyya dai sun sanar da kamo mutanen da su ka kai harin ta’addanci akan ‘yan shiyar da ke juyayin Ashura a wani kauye da ke gabacin kasar, tashar talbijin ta Saudiyya ta ambato majiyar tsaron kasar na cewa; an kame mutane tara wadanda su ka kai harin a yankin Ihsaa da ke gabacin Saudiyya a daren jiya wanda ya yi sanadin shahadar mutane bakwai  da jikkata wasu, mafi yawancinsu kananan yara.
Bugu da kari majiyar ta ce; mutanen sun shirya kai wasu hare-haren a cikin garuruwan Khubar da Qatif da ke gabacin kasar inda mafi yawancin mutanensa ‘yan shi’a ne, harin na jiya ya zo ne dai a lokacin da ake rayuwa cikin zullumi a  gabacin Saudiyya din, bayan yanke hukumcin kasa da wata kotun kasar ta yi wa daya daga cikin fitattun malaman shi’ar kasar.
1470716

Abubuwan Da Ya Shafa: Kasem
captcha