
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na Islamentifo cewa babban malamin yahudawan Isra’ila Khakham Isaac Yusuf ya bayyana cewa yahudawa masu tsatsauran ra’ayin sahyuniya da suke keta alfarmar masallacin quds suna aikata babban laifi.
Rahotanni sun ce wasu yahudawa sahyuniya 'yan kaka gida masu tsatsauran ra'ayi dauke da bindigogi sun banka ma wani masallaci wuta a kauyen Al-mugir da ke yankin gabar yamma da kogin Jordan, inda suka kone shi kurmus.
A nasu bangaren jami'an gwamnatin kwarya-kwarya cin gishin kai ta Palastinawa sun ce yahudawan sun killace masallacin ne suna dauke da makamai, ta yadda Palastinawan da ke wurin ba za su iya tunkararsu ba, inda suka banka wuta kan masallacin tare da cikakkiyar masaniya daga jami'an tsaron Isra'ila, wanda kuma ba shi ne karon farko da suke yin hakan ba a wannan kauye, inda a cikin dubu biyu da sha biyu sun kone wani masallaci a wurin baki daya.
Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin 'yan kwanakin nan dai yahudawan sahyuniya suna kai farmaki kan yankunan palastinawa da ke gabacin birnin Qods da kuma gabar yamma da kogin Jordan, inda suke kone masallatai da kuma makarantu gami da kaddarorin palastinawa, kamar yadda jami'an tsaron yahudawan na Isra'ila suke bi gida-gida suna kame matasa da ba su gani ba.
1472566