Ahmadi yana cewa ra’ayin hadin kai tsakanin sunni da shi’a, kusan shi Ahmadi din ne ya gabatar dashi ta hanyar juyin juye halin musulunci,kuma muhimman malamai masu fada aji na musuluman duniya, sun yi cikakken maraba da ra’ayin.
Da yake nuna sanadiyan da ya janyo nasarar juyin juye halin, cewa yayi al’ummar Iran suna da zurfin imani da ka’idodin mulunci. Akan wannan imani aka samu gagarimmin shiga a matsayi dabam dabam na juyin juye halin.
A fadarsa, “wani muhimmin sanadi shi ne, mutane sun bi ummurnin shugaban juyin juye halin.”
Shugaban al’adun gargajiyar Iran na Qatar ya kara da cewa, ta yadda za’a iya tabbattar da zaman lafiya da ci gaban juyin juye halin shi ne, a kokarta wurin bunkasa imani tsakanin mutane, musamma ma matasa.
Yana jawo hankalin mu da cewa juyin juye halin musulunci shi ne ya kaddamar da sabon tsarin gwamnati a duniya wanda ya saba wa tsarin kwaminisanci da jarin hujja. Ya kuma kara da cewa wannan sabon tsari, wanda yak e dogaro da mazahaban musulunci na marigayi Imam Khomeni,ya samu karbuwa a wurin maneman ‘yanci a duniya, musulumai da wadan da ba musulumai ba.
Iraniyawa suna bikin cika shekara talatin da nasaran juyin juye hali a cikin asubahin kwana goma, daga daya ga watan Feburero zuwa sha daya.
357695