Yan wasan kwaikwayo na Oman da Sudan da Iraqi sun yi wasanni 48, wadan da jigun su shi ne juyayi ga ‘yan yaran Gaza.
Abdul Ra’uf Sham’un, darakton nune nunen, ya fada wa Almenar cewa kisan gillar da aka yi wa yaran Gaza da shan wahala da matsalar Falisdinawa a cikin mummunar harin kwana 22 da Yahudawa suka kai wa Falistin, tare da rushe rushen gidaje da muhimman gine gine sa’an nan da nuna bajintar da Falisdinawa suka yi , sune muhimman jigun wasannen da aka yi.
Jihad Alameri, dan wasan kwaikwayon Jordan, yace nuna wasan kwaikwayo kwakkwarar hanya ce ta arangama da mahaukacin makiyi marasa imani.
Nune nunen nan, mai suna “juyayi ga ‘yan yaran Gaza” za’a cigaba dashi har ran Laraba, 4 ga Feburero. Sa’annan zane zanen da aka baje duk za’a sayar dasu ne a cikin sauki don albarkacin mutanen Gaza da aka kuntatawa.
356719