IQNA

Kaddamar da kasuwar baje kolin wakoki ta kasa da kasa ta nuna goyan baya ga Gaza a Kasar Mauritaniya

Bangaren hulda ta kasa da kasa: Kasuwar baje kolin ta kasa da kasa ta mawaka masu nuna damuwa da halin da mutanan Gaza ke ciki . A jiya ne 15 ga watan Bahman aka fara tare da halartar mawaka daga Mautiniya da kuma kasashen Larabawa da na sauran Afrika a birnin Nuwakcott babban birnin kasar ta Mauritaniya.
Cibiyar koyar da Alkur'ani ta Iran Iqna bayan nakaltowa daga gidan Talbijin din Almanar ya watsa rahoton cewa: a wannan kasuwar baje koli bayan mawakan akwai da dama daga masana da masu kare hakkin dan adam day an siyasa dam asana al'adu daga kasashe daban-daban na duniya.
Sami Alhaj shugaban bangaren kare hakkin dan adam na gidan talbijin na Aljazira da Abdul Bari Atwan shugaban Jaridar Alkudus Al'arabiya da ke fitowa a birnin London da wasu mawaka 20 fitattu daga kasashen larabawa na daga cikin baki na musamman a wannan kasuwar baje koli.
Muhamman Walid Idum mamba a komitin sa ido kan shirye-shiryen wannan kasuwar baje koli ya bayyana cewa:kasuwar baje kolin wakoki a Mauritaniya karkashin gayyatar Muhammad Walid Bamba shugaban mawakan wannan kasa an shirya ne da burin jinjinawa yan gwagwarmaya al'ummar gaza tare da goyan bayan mutanan wannan yanki da aka zalumta ba tare da kariya ba.Ya kara da cewa Mawaka da suka halarta sun yi wakoki da suka shafi goyan baya ga Gaza day an gwagwarmaya Palasdinawa da yin Allah wade da kisan gilla ga mutanan yankin da sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi daga karshe sun kara nuna goyan bayansu ta ruhi da ta dukiya ga Mutanan Gaza. Da kuma nuna hotunan harin dabbanci na kwanaki 22 da Isra'ilata yi kan Gaza tare da kasha mata da kananan yara.

359317