Bangaren yan jarida/Muhammadu Daryabi: Bangaren kula da Kansarki a garin Khuramshahr sun bada kautar tambarorin da ke dauke da hotunan jagora a sansanin Nabar a tsawon shekaru takwas na lokacin yaki ga gidan ajiyar kayayyakin tarihi na Hiroshima.
Cibiyar koyar da Alkur’ani ta Iran Iqna daga Khurramshahar ta watsa labarin cewa: wadannan tambarori an tsara su ciki sha’awa da kuma suka hada manyan hotunan Jagora a lokacin shekaru takwas na kare juyin juya halin musulunci inda aka bada kautar su ga gidan ajiyar kayan tarihi na Hiroshima.Har ila yau an bada kautar wasu hotunan da suka shafi ta’addancin tsohon shugaban kasar Iraki Saddam day a aikata kan al’ummar Iran.
Gidan ajiyar kayan Tarihi na Hiroshima shi ne gidan ajiyar kayan tarihi na farko day a sami irin wannan kauta mai girma.
An taba bawa jami’ar Azzahar tambarorin da ke dauke da hotunan Imam Khomeini ® kuma an tsara sun e a Khurramshahar da ke nuni da hanyoyin gwagwarmayar Imam Khomeini a kan tafarkin musulunci da koyarwa ta Annabi muhammadu.
Nan bad a jimawa ba za a aika irin wadannan Tambarori na jagora da gidajen ajiyar kayan tarihi fitattu a kasashen duniya daban-daban.
359636