Bangaren siyasa:Kuski daya daga cikin manyan masana a cikin Iran ya bayyana : a cikin shekaru talatin na juyi ,Iran ta samu ci gaba ta fuskoki daban-daban musamman kere-kere amma mafi muhimmancin kauta da ci gaba da juyin musulunci ya bawa al'ummar Iran shi ne yancin siyasa.
Mahamad Sadik Kushki mamba a kungiyar malummai a jami'ar Khajja NasrulDine Tusi a tattaunawa da cikbiyar koyar da Alkur'ani ta Iran Iqna kan juyin musulunci shi ne babban nasara da abu mai muhimmanci day a wakana a karni na 20 ya bayyana cewa: Tasirin juyi a ciki da wajen Iran ya kawo daidaito a tsakanin jama'a. ya kuma ce sauye-sauye da canji da juyin musulunci ya kawowa duniya ya bayyana a fili karara da cewa: a lokacin da danniya da wariya iri iri ya mamaye duniya a wannan lokaci da masu raya raba addini da siyasa sai juyin musulunci ya bayyana a Iran da nunwa yan yammaci kuskuransu.
Wannan malamin Jami'a ya kara da cewa; juyin musulunci ta hanyar dogaro da kai da akidar musulunci da jagorancin Imam da Jagora juyi ya isar da manufa ta hakika ta addini a matsayin babban abin riko da zai isar da dan adam ga kololuwar ci gaba.
360574