Bangaren Zamantakewa:Shugaban Cibiyar kula da Al'adu da Binkasa Musulunci a rana 19 ga watan Bahman ne a bukukuwan bude taron bincike kan yadda aka zartar da dokokin da suka shafi Iyali a kasashen musulmi ya yi bayani kan Aya ta 21 a cikin Suratul Rom da yadda ta bawa Gina Iyali muhimmanci a musulunci.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ta watsa rahoton cewa: Hujjatul Islam da musulmi Ali Akbar Rishad shuagaban cibiyar al'adu da binkasa addini a lokacin bude wannan taro kan binciken yadda aka zartar da dokokin da suka shafi iyali a kasashen musulmi a babban dakin taron ma'aikatar noma ya yi bayani kan aya ta 21 a cikin suratu roma da ta yi bayani kan muhimmanci iyali da nuna kauna da sauyaya a tsakanin juna da cewa wannan shi ke bayani kan muhimmancin da addini ya bawa iyali.
Ya kara da cewa: tushen halittar mata shi ne gina iyali kamar yadda tushen halittar dmutum ,sammai da kassai alamomi ne na ayoyin Allah . Kan la'akari da haka gina iyali abu ne mai girma da daraja matuka kuma dole a kiyaye haka a tsakanin mata da maza.risha ya kara da cewa sulhu da kwaciyar hankali na daya daga cikin muhimman abubuwan day a kamata a yi la'akari da shi kamar yadda Alkur'ani ya yi nuni da cewa shi ne tushen aure a tsakanin mace da namiji da ta hanyar gina iyali ne za a isa ga kamala.
360584