Banagaren Labarai: Said Hakani: Bukin tunawa da shekaru 30 na nasarar juyin juya halin Musulunci a a bangaren kula da al'adu na jamhuriyar Musulunci a garin Salzburg na kasar Ostriya.
Bangaren labarai na cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna bayan ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na hukumar al'adu ta Iran ya watsa labarin cewa: wannan bukukuwa an fara su ne bayan karatun alkur'ani mai girma inda hujjatul Islam da musulmi Said Musa Huseini limamin masallacin Ahlulu Beit (AS) bayan nuna farin ciki da ranekun nasara na juyin Musulunci ya fara bayani dalla-dalla kan juyin Musulunci na Iran .
Shi ma Kiyarshi shugaban ofishin hukumar kula da al'adu a kasar Ostriya ya bayyana irin nasarorin da Iran ta samu bayan juyi a cikin shekaru 30 a daidaiku dama al'ummar Iran baki daya.
360420