Bangaren Labarai/Said Hakani: Masanasa a kasar Rasha sun dukufa kan binciken nasarorin da juyin juya halin Musulunci a Iran ya jawowa kasar a cikin shekaru talatin.
Bayan da cibiyar koyar da Alkur'ani ta Iran Iqna ta nakalto daga daga babban bangaren hullda da jama'a na hukumar kula da al'adu ta watsa rahoton cewa: Garanet Awanric da Iskaniya malumman jami'o'in Masko da Padid a kasar Rasha sun rubuta wata makala da take bayani kan tarihin juyin juya halin Musulunci a Iran da cewa a yau duk da makiya a ciki da wajen kasar ta Iran ,kasar ta na ci gaba da kalubalantar zalumci da danniyar manya kasashen duniya da kuma samun ci gaba mai yawa. Daga karshe sun bayyana cewa Iraniyawa a ciki da wajen kasar sai kara nuna adawa suke yi da mulkin mallaka da danniya.
360415