Bangaren al'ada:Fina-finan Yammaci karkashin makircin Yahudanci na yi wa Musulunci mummunan tunani da hakan ya samu asali a tsawon tarihi.
Azizullah Haji Mashhadi mai lura da tsara fina=fina ya yi nuni da wannan matsala ta mummunan tunani kan Musulunci a fina-finan yammaci inda ya bayyana cewa: fina-finan yammacin Turai dagangan suka bari aka shirya da watsa film din Haliyord saboda tasirin Yahudawa da yadda suka kankamai komi da komi a yammacin Turai duk da cewa sun san irin mummunan abubuwan batanci kan Musulunci da film din ta kumsa. A lokacin da yake amsa tambayar ko bay a ganin akwai bangaren siyasa cikin lamarin sai ya kada baki y ace: yan siyasa a yammaci sune ke jan akalar lamura da suka shafi al'adu da kwarewa inda ya shafi finafinan cikin gida amma lamari kamar wanda ya shafi Musulunci akwai sa hannun yahudawa da makiyan addini a irin wadannan kasashe ko shakka babu.
360478