Bangaren kasa da kasa: A karo na biyu an fara gasar harder hadisan manzon Allah karo na biyu a Hadaddiyar daular Larabawa a ranar 18 ga watan Bahman a cibiyoyin harder Alkura'ani mai tsarki a birnin Abu Zabi babban birnin kasar a gasar Jabir bin Rashid Alhami.
Cibiyar Koyar da Alkur'ani a nan Iran Iqna bayan ta nakalto daga jaridar Hadaddiyar daular larabawa Alkhalij ta watsa rahoton cewa;Ali bin Jabir Alhami shugaban shirya wannan gasa a wannan karo ya bayyana cewa: wannan gasar an shirya tan e karkashin sa idon cibiyar harder Alkur'ani ta Abu Zabi da sauran hukumomi da cibiyoyin da suke kula da sha'anin addini a kasar.Ya kara da cewa: wannan gasar ta hada yan takara 650 da aka kasa su gida biyu bangaren mata da kuma bangaren maza kuma mahardatan sun hardace hadisai 15 wasu 125 wasu 100 wasu 60 da kuma 40 kuma za a kwashe kwanaki uku ana gudanar da wannan gasar. Wannan ya zo na daya zai samu kyauta mai coka da allon girmamawa.
360418