Bangaren kasa da kasa: Kasuwar baje kolin ta'addancin HARAMTACCIYAR KASAR ISRA'ILA kan al'ummar Gaza da aka fara a ranar 18 ga watan Bahman a Girma tare da halartat kwararru daga Labanon da Girka.
Cibiyar koyar da Alkur'ani ta Iran Iqna ce ta watsa rahoton cewa: Kwararru dam asana daga kasashen Labanon da Girka sun baje kasuwar bayyana ta'addancin HARAMTACCIYAR KASAR ISRA'ILA kan al'ummar Gaza da yadda al'ummomin Palasdinu ke fuskantar matsaloli da gallazawa daga HARAMTACCIYAR KASAR ISRA'ILA da kuma yadda suka yi wa fararen hula kisan kiyashi da ya hada mata da kananan yara.Akwai kuwa hotuna da suke nuni da yadda masallacin kudus yake ciki da kuma yadda aka gina katanbgar zalumci da ta raba al'ummomin Palasdini da killace su a yammacin kogin jodan da wannan ma ke nuni da wani bangare na ta'addancin HARAMTACCIYAR KASAR ISRA'ILA .Har ila yau akwai tarihin mamaye Palasadinu da gwamnatin HARAMTACCIYAR KASAR ISRA'ILA ta yi sai kuma bangaren kayan hannu da Palasdinu suka yi .
360441