Bangaren kasa da kasa : Muhammah Said Tantawi babban malamin Jami'ar Azhar a kasar Masar da Ruwan Williams shugaban kungiyar kiristocin Angalika ta duniya sun jadda goyan bayansu ga tattaunawa Addinai da nufin fahimtar juma.
Cibiyar Koyar da Alkur'ani Iqna ce ta watsa labarin cewa: Jaridar Alwatan da ake bugawa a kasar saudiya ta bada labarin cewa; Said Tantawi shugaban jami'ar Azhar da Rawan Williyamz sun sanar da goyan bayansu kan duk wani kokari na fahimta juna da tattaunawa tsakanin addinai da hakan zai iya taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya ko shakka babu kuma wannan shi ne tushe duk wani goyan bayan da taimakaon juna da kuma zai tabbatat da sulhu da kwaciyar hankali a duniya .Tare jaddada matakinsu da kuma fatar ganin wasu ma sun yi ko yio da hakan.
361231