IQNA

Za a kaddamar da hanyar dogo a tsakanin Makka da Madina

Bangaren kasa da kasa: shirin kaddamar da layin jirgin kasa mai tsananin gudu tsakanin Makka da Madina da zummar kawo sauki a tsakanin masu zirga zirga a biranan biyu za a fara a karshen wannan shekara.
Cibiyar koyar da Alkur,an ice a Iran Iqna ta watsa labarin bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta kasa da kasa IINA da ke saudiya cewa: tuni aka kamala shirye-shiryen farko na fara wannan aiki mai matukar muhimmanci na hada layin dokon na jirgin kasa mai tsananin gudu a tsakanin biranan biyu duk a cikin kokarin kawo sauki ga maniyata da masu bulaguro a tsakanin wadannan biranai masu matukar daraja da matsayi a guraren musulmi na duniya .Kuma a shekara ta 2013 ne za a kawo karshen wannan aiki na gina layin dogo mai tsawon kilometa 360 a cikin sa'a guda da rabi kacal kuma za a kawo tsaro ga maniyata aikin hajji.

361181