IQNA

Taron sake gina Gaza ta hanyar bada taimako a nan Tehran

Bangaren Zamantakewa: Murtada Tadamun daga cikin wadanda suka shirya wannan taro ya bayyana cewa:tara taimako don sake gina Gaza abu ne mai kyau kuma za su gudanar da tarorrukan ne a nan Tehran bayan bukukuwan nasarar juyin musulunci a Iran.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a nan Iran Iqna ce ta watsa labarin cewa: Gwamnan birnin Tehran Murtada Tamddun a zaman tunanin sake gina Gana da yadda za a tara kudade ya bayyana cewa sake gina gaza wani abu ne mai matukar muhimmanci da alfano kuma za su shiga cikin aikin tara kudaden taimako gadan-gadan bayan bukuwan ranekun tunawa da nasarorin juyin juya halin musulunci da ake yi a fadin Iran da wajenta bayan shekaru 30 .daga karshen ya bayyana cewa; al'umma a lokacin yaki da bayan yakin sun nuna goyan bayansu ga al'ummar gaza da yi wa gwamnatin Gaza Allah wadai da ta'addancin da suka aikata kan zirin gaza.

361171