Bangaren Yan Jarida: Muhsin Ma'amuli:Ayatullah Musawi Ardabili a lokacin ganawarsa day an makaranta a Ardabil ya bayyana masu cewa: Makomar al'umma tana hannun matasa na Gari masu kishin kasa da al'umma.
A wani rahoto da cibiyar koyar da Alkur'ani a nan Iran Iqna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Hauza ta bayyana cewa: wani gungun yan makaranta yan yankin Ardabil sun ganada ayatollah Ardabili.Ayatullah Musawi Adabili a lokacin wannan ganawa ya bayyana cewa:Matasa sun taimaka da taka rawar gain lokacin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran kuma wadanda suka yi shahada daga cikinsu har yanzu sunayen na zagayawa a tsakanin al'umma . Dangane da makomar al'umma tana hannun matasa na gari ya kara da cewa: dole mutum ya aikata aikin alheri a lokacin kurciya da sarmintaka musamman a lokacin neman ilimi domin ta haka neb a za a manta da shi ba a tsakanin takwarorinsa a cikin al'umma. Ya kara da cewa kafin nasarar juyin juya halin musulunci matasa bas u da cikakkiyar masaniya kan Alkur'ani da bukukuwan addini domin ba ailmantar da sub a ko kuma sun ki su ilmantu da haka amma a yau lamarin ba haka yake ba an samu matasa masu imani da dogaro da addini da koyarwa ta Alkur'ani da dogaro da kai.
361579