IQNA

Nuna Gudummuwar Mata Lokacin Nasarar Juyin Musulunci A Taron Calus

Bangaren siyasa da zamantakewa:Saboda tunawa da shekaru talatin da nasarar juyin musulunci a iran banagren al'adu a ofishin yada aadini a yankin calus an gudanar da wani taron nuni da rawar da mata suka taka a nasarar juyin musulunci a Iran.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ce ta watsa labarin cewa: a yankin Mazandaran Rida Muhir Ali Zade masani kan harkokin da suka shafi al'adu a ofishin yada addini a Calus a lokacin gudanar da taron sanin irin rawar da mata suka taka lokacin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran ya bayyana cewa; tarbiyartarwa da al'umma ta samu tushe ne daga mata kuma ya taimakawa a rayuwar zamantakewa da ci gaban al'umma gami da wayewarta.Ya kara da cewa: rawar da mata suka taka a vikin gwagwarmayar samara da juyin musulunci abin ya wuce misali da tunani domin kuwa da a ce bas u taimaka ba a lokacin yakin shekaru takwas dab a haka lamarin ba kuma sun zama abin koyi a sauran al'ummomi a nan gaba. Mihr Ali Zade ya fito fili ya bayyana cewa: wadanda suka taimaka wajen samun yanci mata ne kuma sun taka muhimmiyar rawa kuma mata a kullum sun e ke nunawa yayansu hanyar da ta dace su bi da goyan bayansu a kullum dare da rana.

362134