Bangaren Kasa da kasa: Mahalarta taron kasa da kasa na kafafen watsa labari masu yancin fadin albarkacin baki da yaki da cin zarafin addinai da aka gudanar a birnin San'a babban birnin birnin kasar Yaman sun wajabta kafa komitin da ya hada marubuta,Kafafen watsa labarai,malumman addini dam asana musulmi da za sun shirya tsarin na bai daya na gwagwarmaya da cin zarafin abubuwa masu daraja a musulunci.
Bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Alsahawa net cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ta watsa rahoton cewa: mahalarta taro a marecen litinin sun fitar da bayanin bayan taro da ta bukaci bincike daga tushe kan dalilai cin zarafin addinin musulunci a kasashen yammacin Turai kuma makiya addinin musulunci da musulmi sun sabawa dokokin kasa da kasa.Har ila yau a cikin wannan bayani sun tabbatar da wajibcin aiki kafada da kafada da juna da tuntubar juna a tsakanin cibiyoyin farfaganda da al'adu a kasashen musulunci domin kare addinin hahakin musulunci da ilmantar da wadanda ba musulmi ba addinin musulunci.Bada amsa da tambayoyin batanci da rudani ga addinin musulunci . Mahalarta taron na Yaman sun bukaci jami'o'in msulunci sun fada matsayinsu wajen kare addini da bada amsoshi da kalubalantar masu maganganun batanci ga Addinin musulunci.
362201