IQNA

Za a Kaddamar Da Shirye-shiryen Aikata Alheri Da Hani Da Haramun A Ilmance

Bangaren zamantakewa: A yau ne a jami'ar da ke kula da mazhabobin da dariku a Musulunci za a far taron Kaddamar Da Shirye-shiryen Aikata Alheri Da Hani Da Haramun A Ilmance .
Cibiyar koyar da karatun Alkur'ani a Iran Iqna ce ta watsa labarin cewa: kafin bude babban taron ,za a fara ne da taron manema labarai da zai yi bayani kan burin kaddamar da wannan taro na farko kan hanyoyin karfafa guiwar aikata abubuwan alheri da kuma a bangare daya da hani da duk wani aikin assha da Allah ya hana kuma za a kaddamar da rahoto kan ayyukan da wadanda suka shirya taron suka gudanar.Hujjatul Islam da muslim Biazar Shirazi shugaban jami'ar da ke kula da mazhabobi a musulunci a wannan zaman taron zai kasance daga cikin wanda zai amsa tambayoyinmanema labarai da kuma abubuwan wannan taro na kwanaki biyu zai kumsa.

362192