IQNA

Musulmin Tailand Sun Fara Shirye-shiryen Taimakawa Gaza

Bangaren Zamantakewa: Matasan Musulmin Tailand a wani matakin jinjinawa sun kaddamar da shiri na musamman na taimakawa mazauna yankin Gaza kuma za su saida kayan sanyawarsu don taimakawa mutanan Gaza.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ce ta watsa rahoton cewa: A wata hira da shugaban hadin gwiwar matasa musulmi a jami'ar Maha Nakhan a kasar Tailand ya bayyana cewa: kungiyoyin matasa yan jami'a a wannan kasa sun yi niyar taimakawa yan uwansu musulmi da aka zalumci a Gaza bayan harin ta'addanci na kwanaki 22 da gwamnatin Haramtaciyar kasar Isra'ila ta kai masu day a yi sanadiyar shahadar daruruwa da jikkata wasu dubbai da kuma tusa wasu dubban cikin mawuyacin hali na rashin muhalli da kuma sauran matsaloli da masu yawan gasket kum.Kuma ya zuwa yanzu sun tara kusan kudin kasar dubu 71500 da nan ba da jimawa ba za a tura zuwa Yankin Gaza.

362250