Bangaren Al'adu da kwarewa: Littafin Sahifa Sajjadiya day a kumshi addu'o'I 50 da bukatu 15 daga cikin Addu'o'in Imam Sajjad (AS) an fassara zuwa yaren Ship a yankin Balkan.
Haji Salim Istafa daga cikin malumman kasar Albani da suka yi fice shi ne ya fassara wannan littafi mai safahohi 515 zuwa wannan jaren na Ship .Ya jaddada cewa : ya fassara litattafai da makaloli masu yawa a Hauza da cibiyoyin Addini daga harshen Larabci zuwa harshen Ship.Kuma yana daga cikin komitin malumman koyar da Alkur'ani a Albaniya kuma ya fara fassarar ne a watan Aban na shekara ta 1386 zuwa watan Farvardine na shekara ta 1387 Kuma tuni littafin ya samu karbuwa daga Yan shi'ar Albaniya.
362224