Bangaren Alkur'ani: Wani Mahardacin alkur'ani ya tabbatar da wajibcin tarbiyartar da masu tabligi kan Alkur'ani musamman wadanda ake tura zuwa kasashen waje da yin tabligi kan Alkur'ani a fadin duniya da cewa: A samara da wani shafi da sansani na musamman karkashin hukumar al'adu da dangantaka ta musulunci da hakan zai taimaka wajen sanin Alkur'ani a cikin kasashen duniya.
Said Mahdi Fadiniyan Alkalin mahardata Alkur'ani na kasa da kasa kuma mahardacin Alkur'ani a wata hira da cibiyar Alkur'ani ta Iran Iqna ya bayyana cewa: Yadda ake da mahardata masu yawa a cikin Iran da sauran yan uwansu a kasashen duniya yana da kyau a samara da wani shafi da za a rika tattaro labarai day a shafi mahardata. Ya fito fili ya kara da cewa:Wannan hukuma za ta iya samara da Shafin Internet na mahardata da binkasa hanyoyin da za taimaka masu da cimma moriyar abubuwa da suka karanta na Alkur'ani mai girma da daukaka.
362258