IQNA

Jagoran yan shi'a a Pakistan: Ya yi Kashedi Kan Hadin Kai da Tsaron Kasa

Bangaren Manema Labarai:Said Fadini Nush Abad: shugaban yan shia'n Pakistan ya fitar da bayanin Allah wadai da kisan kiyashi na dabbanci kan yan shi'ar Pakistan da cewa wannan lamari na barazana ga hadin kan kasa da tsaronta.
Bangaren manema labarai na cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Hauza ta watsa rahoton cewa: Allama Said Sajid Ali zakawi shugaban yan shi'ar Pakistan a cikin wannan bayani ya jaddada nauyin day a rataya a wuyan mahukumtan kasar na kare hakkin yan kasa da addininsu kuma nauyi ne ga jami'an tsaro ,sojoji da yan sanda na su kare al'umma a duk inda suka taru don gudanar da wani abu day a shafi rayuwarsu da addininsu.Ya kara da cewa: abin ciza yatsa ne kan abun da ake gain yana faruwa a kasar na kisan kiyashi da gilla a harin ta'addanci kan fararen hula . Ya kamala jawabinsa da cewa: kafin haka ta faru mun shaidawa mahukumta amma bas u yi aiki da abin da muka shaida masu da yi wa lamarin sako-sako amma ya bukaci gwamnati a cikin gaggawa ta gano da kama wadanda suka aikata wannan aiki tare da hukumta su.

361672