Bangaren Siyasa da zamantakewa:Mahdi Mustafawi mai bawa shugaban kasa shawara kuma shugaban hukumar al'adu da dangantaka ta musulunci ya gana da tattauanawa da takwaransa na kasar Indiya Ambika Suni.
Cibiyar Koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ce bayan ta nakalto daga cibiyar Al'adu ta Iran a Indiya ta watsa rahoton cewa; Ambika Suni ministan al'adu na kasar Indiya a lokacinganawarsa da Said Mahdi Nabiy Zade jakadan iran a da kuma Karim Najafi mai kula da ofishin Al'adu na Iran a Dahli ya yi fatar dangantakar kasashen biyu ta binkasa ta dukan bangarori.Mustafawi shi ma a lokacin ganawarsa da Hasan ya jinjina masa kan jan aikin day a gudanar ta fuskar ilimi,tattalin arziki da siyasar kasashen biyu ya kuma gayyaci ministan al'adun kasar Indiya day a kawo ziyara a Iran ya kuma amince da wannan gayyata. Ministan al'adun na Indiya ya jinjina masa kan rawar day a ke takawa a harkokin kasa da kasa.
362459