Bangaren siyasa da zamantakewa:Hakkin sanya hijabi ga mata musulmi a Karkizistan da kuma goyan bayan wannan wajibci haka a musulunci an fara bincike a dakin taro na Hotel Dastuk a birnin Pishkak babban birnin wannan kasa.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran ce Iqna ta watsa rahoton cewa wannan mataki ya biyo bayan yadda yan makaranta day an jami'a musulmi a wannan kasa suke ci gaba da fuskantar matsaloli saboda suna sanye da hijabi da kuma cangwama a tsakanin yan uwansu da takwarorinsu mata.Babban dalilin wannan bincike shi ne goyan bayan mata da ke sanye da hijabi a makarantu tare da kawo karshen nuna masu karan tsana ko rage yin haka a tsakanin yan uwansu mata kuma wannan taro wakilan kungiyoyin addini day an majalisa karkashin amincewar shugaban kasar ne suka shirya wannan taro kuma ma'aikatar ilimi da tarbiya da kuma majalisa ne suka bada karfin guiwar gudanar da bincike kan hakan.
362372