Bangaren Siyasa Da Zamantakewa:Sheikh Mohammad Yazbak mamba a komitin zartarwa na kungiyar hizbullah ya yi nuni da wannan lamari cewa: Imam Khomeini ® tun farkon kafa jamhuriyar musulunci a iran ya kusanto Palasdinawa da taimakawa wannan al'umma da ake zalumta da kokarin ganin sun samu hakkinsu da jaddada kusancin juyin juya halin musulunci da lamarin Palasdinu tun farko.
Bangaren cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna da ke labanon ne ya bada labarin cewa: Sheikh Yazbak mamba a komitin zartarwa a kungiyar Hizbullah ta labanon a wani taron karawa juna sani a cibiyar Al'adu ta Iran a wannan kasa inda aka samu halartar Muhammad Husein Ra'is Zade shugaban cibiyar da imam Mahir Hamud limamin masallacin Kudus a garin Saida na kuduncin Labanon har ila yau da Marwan Faris dan majalisar dokoki a Labanon ya bayyana cewa: Iran a yau karkashin shugabancin da jagorancin Ayatullah Khamna'I tamkar Iran ta jiya ce karkashin jagorancin Imam Khomeini ® da ke goyan baya da taimakawa Palasdinawa. Har ila yau Yzbak ya yi nuni da adawar da wasu ke nunawa da lamarin wilayatul fakih da cewa irin wadannan mutane yan Koran Amerika ne domin wannan lamari na wilayatul Fakih kan doka yake day a shafi Akhalaki,tsaro da ilimi.
362131